Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Mbappe, Ronaldo, Sancho, Dybala, Wilson, Torres

Kylian Mbappe

Juventus na shirin kashe £360m domin dauko dan wasan Paris St-Germain Kylian Mbappe, mai shekara 21, kuma kungiyar za ta iya bai wa PSG Cristiano Ronaldo, a cewar jaridar (Mirror)

Borussia Dortmund ba ta da niyyar sayar da dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho a watan Janairu, wanda aka dade ana rade radin zai tafi Manchester United da bazara. (Sport Bild, via Mail)

Chelsea na son dauko dan wasan Juventus da Argentina Paulo Dybala, mai shekara 22. (Tutto Mercato Web, via Star)

Kazalika Chelsea ta so dauko dan wasan Barcelona Lionel Messi, mai shekara 33, inda ta nemi biyansa £1m duk mako a cinikin £225m lokacin musayar 'yan kwallon 2014. (Sky Sports)

Cardiff City ta amince da yarjejeniyar dauko aron dan wasan Liverpool Harry Wilson, a yayin da su ma Derby County da Nottingham Forest sue zawarcin dan wasan mai shekara 23. (Football Insider)

Arsenal na son doke Manchester United a yunkurin biyan £35m don dauko dan wasan Villarreal mai shekara 23 Pau Torres a watan Janairu. (Express)

Middlesbrough na yunkurin kammala kulla yarjrjrniya don dauko aron Yannick Bolasie, mai shekara 31, daga Everton. (Sky Sports)

Swansea City na son ta karbi £18m daga wurin Tottenham kan dan wasanta mai shekara 22 dan yankin Wales Joe Rodon. (Telegraph - subscription required)

Dan wasan tsakiyar Manchester United Bruno Fernandes, mai shekara 26, ya musanta sukar kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer da kuma abokan murza ledarsa na kungiyar bayan Tottenham ta doke su da ci 6-1 gabanin tafiya hutu. (Sport TV, via Metro)

Mamallakin Derby County Mel Morris ya ce ba za a kori kocin kungiyar Phillip Cocu ba idan suka sha kashi a hannun Watford ranar Juma'a a yayin da kuma ya musanta rahotannin da ke cewa zai dauko tsohon dan wasan Ingila Wayne Rooney, mai shekara 34, domin maye gurbin Cocu. (Talksport)