Man City vs Arsenal: Abubuwan da suka kamata ku sani kan karawar da za su yi ranar Asabar a gasar Premier League

Manchester City da Arsenal

Ranar Asabar 17 ga watan Oktoba za a ci gaba da gasar Premier League karawar mako na biyar.

Manchester City na fatan cin wasan farko a Etihad a bana, bayan da Leicester City ta ɗura mata 5-2 a gasar Premier League ranar 27 ga watan Satumba.

Arsenal kuwa na fatan cin karawa ta huɗu a wasa na biyar na hamayya da za ta yi a Etihad.

Ana kuma sa ran sabon ɗan ƙwallon da Arsenal ta ɗauka a bana, Thomas Partey zai buga mata wasan farko ranar ta Asabar.

Tun ranar Alhamis ɗan ƙwallon ya fara atisaye, kuma kocin Gunners, Mikel Arteta ya ce ɗan ƙwallon na kan ganiyarsa a shirye yake ya buga tamaula.

City ta yi nasara a kan Arsenal a wasa shida baya da suka kara a Premier League da cin kwallo uku a wasa biyar daga ciki.

Kevin de Bryne ya ci ƙwallo biyar ya kuma bayar da biyu aka zura a raga a gasar Premier League a wasa takwas da ya buga da Arsenal

Kuma biyar ɗin da ya zura a ragar Gunners shi ne wasan da ya ci ƙwallaye a ƙungiya ɗaya a Premier League.

Tun bayan rashin nasara da ta yi a hannun Brighton a watan Yuni, ba wata kungiya da ta haɗa maki da yawa a gasar Premier League kamar Arsenal mai 25.

Arsenal tana mataki na huɗu a kan teburi da maki tara, ita kuwa City tana ta 14 a ƙasan teburi da maki huɗu, bayan wasa uku.

Wasa biyu baya da suka kara a gasar Premier League:

Ranar Laraba 17 ga watan Yunin 2020

 • Man City 3-0Arsenal

Lahadi 15 ga watan Disambar 2019

 • Arsenal 0-3Man City

Cikin wasa 46 da suka yi baya, Arsenal ta yi nasara 23, Manchester City da 13 da canjaras 10.

Wasa hudu da Manchester City za ta buga nan gaba:

Champions League ranar Laraba 21 ga watan Oktoba

 • Man City da Porto

Premier League ranar Asabar 24 ga watan Oktoba

 • West Ham da Man City

Champions League ranar Talata 27 ga watan Oktoba

 • Marseille da Man City

Premier League ranar Asabar 31 ga watan Oktoba

 • Sheff Utd da Man City

Wasa hudu da Arsenal za ta yi nan gaba:

Europa League ranar Alhamis 22 ga watan Oktoba

 • Rapid Vienna da Arsenal

Premier League ranar Lahadi 25 ga watan Oktoba

 • Arsenal da Leicester

Europa League ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba

 • Arsenal da Dundalk

Premier League ranar Asabar 01 Nuwamba

 • Man Utd da Arsenal

Mahukun da za su ja ragamar wasan Manchester City da Arsenal:

Alkalin wasa: Chris Kavanagh. mataimakansa: Sian Massey-Ellis da Constantine Hatzidakis.

Alkali mai jiran ko ta kwana: Anthony Taylor.

Wanda zai kula da VAR: Stuart Attwell, mataimakinsa: Andy Halliday.

Wasannin da za a ci gaba a gasar Premier League:

Ranar Asabar 17 ga watan Oktoba

 • Everton da Liverpool
 • Chelsea da Southampton
 • Manchester City da Arsenal
 • Newcastle United da Manchester United

Ranar Lahadi 18 ga watan Oktoba

 • Sheffield United da Fulham
 • Crystal Palace da Brighton & Hove Albion
 • Tottenham da West Ham United
 • Leicester City da Aston Villa

Ranar Litinin 19 ga watan Oktoba

 • West Bromwich Albion da Burnley
 • Leeds United da Wolverhampton Wanderers

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Premier League:

 • Dominic Calvert-LewinEverton 6
 • Heung-min SonTottenham Hotspur6
 • Mohamed SalahLiverpool 5
 • Jamie VardyLeicester City 5
 • Callum WilsonNewcastle United 4
 • Neal MaupayBrighton & Hove Albion4
 • James RodriguezEverton 3
 • Jorginho Chelsea 3
 • Danny IngsFC Southampton 3
 • Harry KaneTottenham Hotspur3
 • Sadio ManeLiverpool 3
 • Ollie WatkinsAston Villa 3
 • Wilfried ZahaCrystal Palace 3
 • Alexandre LacazetteArsenal FC3
 • Jack GrealishAston Villa 3
 • Patrick BamfordLeeds United 3