Real Madrid: Wasa biyar za ta buga a Oktoba har da El Clasico cikin kwana 15

Real Madrid

Real Madrid za ta buga wasa biyar a cikin watan Oktoba har da El Clasico da karawa biyu a gasar Champions League cikin kwana 15.

Real za ta fafata a wasan farko a bana a gasar Champions League a karon farko a Alfredo Di Stéfano a cikin watan Oktoba da karawa uku a La Liga har da El Clasico da kuma wani wasan a kofin Zakarun Turai.

Wasan farko da Madrid za ta yi shi ne a gida da Cadiz ranar Asabar 17 ga watan, bayan kwana hudu tsakanin Real za ta fara gasar Champions League a gida da Shakhtar Donetsk ranar Laraba 21.

Kuma shi ne karon farko da filin wasa na Alfredo Di Stéfano zai karbi bakuncin gasar Champions League.

Madrid za ta yi wasa biyu a waje a jere da ya hada daya a gasar La Liga da kuma a Zakarun Turai.

A na La Liga shi ne wanda za ta ziyarci Camp Nou a wasan hamayya na El Clasico, kuma na farko a bana a karawar mako na bakwai a gasar ta Spaniya.

Daga nan ne za ta buga wasan Champions League na bana na farko da za ta je waje wato gidan Borussia Mönchengladbach da za su kece raini ranar 27.

A makon karshe na watan Oktoba, Real Madrid za ta dawo gida wato filin Alfredo Di Stéfano, domin buga wasan La Liga da Huesca, sabuwar kungiyar da ta hau gasar Spaniya.

Wasannin da Real Madrid za ta buga zuwa karshen oktoba:

Ranar Asabar 17 ga watan Oktoba

  • Real Madrid da Cadiz

Ranar Laraba 21 ga watan Oktoba

  • Real Madrid da Shakhtar Donetsk

Ranar 24 ga watan Oktoba

  • Barcelona da Real Madrid

Talata 27 ga watan Oktoba

  • Borussia Mönchengladbach da Real Madrid

Ranar 31 ga watan Oktoba ko kuma 1 ga watan Nuwamba

  • Real Madrid da Huesca