Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Ozil, Pogba, Rudiger, Shaqiri, Coman, Jorginho

Mesut Ozil

Dan wasan Arsenal dan kasar Jamus Mesut Ozil, mai shekara 31, ya ki amsa tayin tafiya kungiyar da ke buga gasar Lig ta Saudiyya inda za a rika biyansa £200,000 duk mako. (Fabrizio Romano, via Express)

Shi kuwa dan wasan Manchester United da Faransa Paul Pogba, mai shekara 27, yana son tafiya Barcelona a bazara mai zuwa. (Mundo Deportivo, via Sun)

Dan wasan bayan Jamus Antonio Rudiger, mai shekara 27, ya ce yana son komawa kan matsayinsa a Chelsea bayan yunkurin da ya yi na barin kungiyar a bazarar da ta wuce ya ci tura. (Athletic - subscription required)

Dan wasan Manchester City da Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, ba shi da niyyar tafiya Italiya duk da zawarcinsa da Inter Milan ke yi masa. (Fabrizio Romano, via Sports Illustrated)

Chelsea za ta soma tattaunawa a kan sabunta kwangilar dan wasan Italiya mai shekara 28 Jorginho, wanda aka ce zai tafi Arsenal da bazara. (AreaNapoli, via Express)

Tsohon kocin Juventus Max Allegri zai bi sahun masu son maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer idan Manchester United ta sallame shi. (Express)

Dan wasan Liverpool da Switzerland Xherdan Shaqiri, mai shekara 29, ya ce ya zabi ci gaba da zama a kungiyar a lokacin bazara, duk da rahotannin da ke cewa zai kama gabansa. (Mail)

Manchester United ba ta nemi dauko dan wasan Bayern Munich da Faransa Kingsley Coman, mai shekara 24 ba, a lokacin musayar 'yan kwallo na bazara, a cewar daraktan wasanni na kungiyar ta Jamus Hasan Salihamidzic. (Bild, via Mail)

West Brom ta amince da £15m kan dan wasan Huddersfield dan kasar Ingila mai shekara 23 Karlan Grant. (Sky Sports)

Juventus ta bi sahun Manchester City da Bayern Munich wajen zawearcin dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 28. (Sportmediaset, via Manchester Evening News)

Liverpool za ta bari Harry Wilson ya sake tafiya zaman aro, amma ta ki amincewa da tayin Swansea City na daukar dan wasan mai shekara 23. (Athletic, via Wales Online)

Wilson na cikin 'yan wasa biyar da Liverpool take son sayarwa. (Express)