SARS: Rukunin mutane biyar da suka sa zangar-zangar #EndSARS ta yi armashi

Masu raba abinci suna taka rawa sosai
Bayanan hoto,

Masu raba abinci suna taka rawa sosai

Zanga-zangar kyamar SARS ta shiga mako na biyu a wasu sassan Najeriya ciki har da Abuja, inda ake kallonta a matsayin wata fafutukar neman kawo sauyi a tsarin 'yan sandan kasar mafi yawan al'umma a Afirka.

A yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zangar da gangami, ana iya ganin matasa dauke da kwalaye wadanda aka yi rubuce-rubuce daban-daban da ke neman a kawo karshen #EndSARS, ko da yake wasu na neman a biya musu wasu bukatun bayan da gwamnati ta rusa rundunar ta SARS wadda ta yi aikin yaki da fashi da makami.

Wannan fafutuka dai ta ja hankalin kasashen duniya, musamman ma fitattun mutane irin su 'yan kwallon kafa, da taurarin fina-finai da dai sauransu.

Sai dai wani abu da ya ja hankalin mutane game da masu zanga-zangar shi ne yadda masu yin ta ba sa nuna gajiyawa sannan sukan share wuraren da suka bata, musamman a birnin Lagos inda ta somo.

BBC ta yi duba kan rukunin mutane biyar da suka sa zanga-zangar ta #EndSARS ta yi nasara.

1. Masu ɗebe kewa

Wannan rukunin na masu zanga-zanga suna zuwa da kayan kida da na kallo inda masu zanga-zanga kan yi ta taka rawa suna shewa. Hakan yana kara musu kuzari da karsashi wajen kara matsa lamba ga gwamnati.

A Lekki, daya daga cikin unguwannin da ake gangamin a birnin Lagos, wasu sukan yi shiga irin ta lauyoyi da likitoci inda suke zuwa wuraren gangamin.

Wani mutum ya zo wurin zanga-zangar a kan babur din nan na alfarma mai suna power bike inda ya rika burge masu gangamin.

Kazalika a unguwar Alausa, wasu sun fito zanga-zanga a kan kekuna da takalma masu daukar hankali. Wani ma yana tuka keke tare da karensa.

2. Masu shewa/zuga

Wadannan kuma su ne mutanen da ke jan ragamar gangamin inda suke bayar da waka ana yi musu amshi, galibinsu maza ne da ke daga jijiyoyin wuya.

Idan babu wannan rukuni na masu gangami, zai kasance lami saboda akasarinsu fitattun mawaka ne da ke da dimbin masoya.

3. Masu ɗaga tuta

Wannan rukunin na mutane ya yi kama da masu debe kewa da mawaka inda suke isar da sakonsu ta hanyar ɗaga tutoci da ke ɗauke da sakonnin da suke son isarwa.

Hotunan wannan rukuni na masu zanga-zanga sun rika yaɗuwa tamkar wutar daji a shafukan intanet.

4. Masu sallah

Wannan rukuni ne na masu zanga-zanga da suke sallah da addu'o'in samun nasara kan abubuwan da suka sanya a gaba. Hakan na nuna cewa duk runtsi ba su manta da ubangiji ba, a cewar wasu da ke sanya ido kan gangamin.

5. Masu shara

Gangami rin wannan yana haifar da kazanta saboda ana ciye-ciyen abinci da abubuwan sha da makamantansu. Don haka wannan kuma rukuni ne na masu zanga-zanga da ke tabbatar da cewa sun tsaftace wuraren da suka yi gangami a duk lokacin da aka bata su.