SARS: Tasirin zanga-zangar matasa don neman kawo sauyi

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Bayan matsi da gwamnatin Najeriya ta fuskanta daga ciki da wajen ƙasar, Sufeto Janar Mohammed Adamu ya rushe rundunar 'yan sanda ta SARS.

Fadar Shugaban Najeriya ta ce ita ce ta bayar da umarnin yin hakan. Sai dai har yanzu masu zanga-zangar neman gyara ayyukan 'yan sandan ba su saurara ba.

A wannan bidiyon na mun duba irin tasirin da matasa masu zanga-zangar suka yi wurin kawo ƙarshen SARS, wadda aka zarga da cin hanci da cin zarafi da azabtar da mutane.