Hotunan gasar dabbobi masu ban dariya na 2020

Hoto daga John Carelli da ke Amurka
Bayanan hoto,

'Mama ki kalle ni - Za iya tafiya a kan ruwa'

Za ka ji kana sha'awar ajiye dabba a gidanka bayan kallon wadannan hotuna, (in baka da ko daya a gida).

Gasar hotunan dabbobi masu abin dariya ta wannan shekarar za ta kawo muku dabbobin da ke abubuwan ban dariya.

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna daga cikin wasu jerin hotunan kyautar:

Sarauniyar barkwanci

Bayanan hoto,

Wata karya da Anne Lindner ta ɗauki hotonta a Jamus

"Ina ganin wani abu mai kyau sama da ka ga karya na hamma," Anne Linder ta rubuta a kan wannan karyar.

Gasar dai a bude take ga duk wani mai kiwon dabba, babu shamaki kan cewa sai mai ƙwarewa kan ɗaukar hoto.

Abin da ake buƙata kawai wasu kudade ne na shiga, tare da wasu ƙirƙire-ƙirƙiren yadda za a iya gabatar da gasar. Ka'idar ita ce ba a yarda ka sanya wa dabbobin kaya ko gilashi ko hula ba.

Hoto daga cikin kwalbar abinci

Bayanan hoto,

Candice Sedighan ta gutsura abinci ta jefa cikin kwalba tare da ajiye iPhone domin daukar wannan hoto

Mene ne ya faru a gaba? Abin taƙaici, ba mu sani ba ko wannan karen ya ci wannan jarrabawa ya iya riƙe kansa.

Wanda ya yi nasarar zai karɓi fam 3,000 da aka sanya kyauta, kuma za a miƙa wa kungiyar Blue Cross mai taimaka wa dabbobi da ke Burtaniya.

Manyan 'yan rawa

Bayanan hoto,

Ian McConnell daga Wales ya dauki 'Edmund' cikin wani yanayin jin dadi

A shirye-shiryen kasuwanci ana cewa ka da ka yi aiki da dabbobi, sai dai wannan magen kamar an halicce ta ne don rawa a kan dandali. Abin barkwanci.

Lokacin hutu ne yanzu

Bayanan hoto,

Akuyar Robert Prat na rayuwa a wani gidan gonarsa da ke gidansa a Sifaniya

Ba abin da za ka gani a nan sai wata akuya zaune a kan lilon hutawa tana tauna ganye. Hutu zalla.

Riƙe da kyau

Bayanan hoto,

Karen Hoglund ya ɗauki hoton Dany da Gabby a cikin mota

Ka da ka kwaikwayi haka a gida! Za mu iya cewa muna da tabbacin wannan karen bai samu horaswa ba kan tuƙi.

Bugu da ƙari Motar a tsaye take.

"Abin da ake iya gani a wannan hoto miji ne da abin ƙaunarsa a zaune a bayan kujera. Ina riƙe da igiyarsu su duka,'' in ji Karen Hoglund daga Amurka.

Killace kai

Bayanan hoto,

Wani kare da aka dauka hoto a Australia a farkon wannan shekarar

Kamar yadda mai karen ya ce, "Wannan ne irin halin da muke ciki a wannan shekarar bayan dokar kullen Covid-19 a fadin duniya".

Doki na musamman

Bayanan hoto,

Daniel Szumilas ya dauki hoton wannan dariyar a Burtaniya

"Dokin ya kama yi mani dariya, lokacin da na koma mota sai na duba madubi ko da wani abu a fuskata," in ji Daniel Szumilas.

Za a sanar da hoton da ya lashe gasar ta wannan shekarar a ranar 19 ga watan Nuwamba.

Dabba mai abin dariya

Bayanan hoto,

Elke Volgelsang ya dauki hoton wannan karya lokacin da ta ke yi kamar wata jaririya

An ceto Noodles daga wajen wani wahalar da dabbobi a Sifaniya aka kuma kai ta Jamus lokacin tana da wata bakwai.

"Wani lokacin tana da abin dariya, ba ta da ɓoye-ɓoye, ƙawa ce ta arziki, ga abin dariya duk da cewa wani lokaci ba ta san tana yi ba," in ji Elke Vogelsang.