Kamaru ta yi watsi da buƙatar sakin Maurice Kamto da 'yan jam'iyyarsa ta MRC

Maurice Kamto, leader of Cameroon Renaissance Movement.
Bayanan hoto,

Maurice Kamto, jagoran Cameroon Renaissance Movement wato MRC.

Gwamnatin Kamaru ta mayar da martani kan wata sanarwar da jami'an kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya suka fitar game da tsare jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto.

Kakakin gwamnatin, Minista Rene Emmanuel Sadi ya ce sun yi la'akari da dokokin ƙasashen duniya da Kamaru ta rattaba wa hannu wajen tsare babban ɗan adawar da wasu magoya bayansa.

A cewarsa, Maurice Kamto ya yi kira ne a bijire wa dokokin ƙasa, da kuma yunƙurin durkusar da madafun iko.

Majalisar Ɗinkin Duniyar ta nemi Kamaru ta cire ɗaurin talalan da ta yi jagoran masu adawa da gwamnatin, kuma ta saki daruruwan wagoya bayansa da gwamnatin kasar ke tsare da su.

Kakakin gwamnatin Kamaru Rene Emmanuel Sadi ne ya bayyana matsayar gwamantin kasar.

Ya siffanta rahoton da cewa na ɓangaranci ne kawai, kuma ya ce da alama MDD ta karkata gefe guda.

"A zanga-zangar da aka yi a ran 22 ga watan Satumba, magoya bayan jam'iyyar MRC 294 ne aka kama a wasu birane huɗu."

Ya kuma ce bayan bincike an saki 176 cikinsu, kuma daga baya bincike ma zurfi ya gano wasu mutum tara cikinsu ne suka kitsa zanga-zangar.

Minista Sadi ya kuma ce Kamaru kasa ce mai aiki da doka da oda saboda haka ne take bin matakan ganin shari'a ta hukunta wadanda aka kama yayin zanga-zangar ta watan Satumba.